An ceto wasu daga cikin 'yan mata 'yan makaranta da ake zargin 'yan bindigar Boko Haram suka sace su ranar Litinin a wata makarantar kimiyya da Fasaha da ke Jihar Yobe.
Gwamnatin jahar Yoben a cikin wata sanarwa da ta fitar tace an kubutar da wasu daga cikin 'yan matan makarantar sakandaren mata ta garin Dapchi da ke Jihar bayan da 'yan Boko Haram suka kai hari a makarantar a daren litinin.
A sanarwar da gwamnatin Jihar ta Yobe ta fitar da sa hanun, darekatan harkokin yada labarai na jahar Abdullahi Bego,Gwamnan jihar Ibrahim Geidam ya jinjinawa bajintar da sojojin Najeriya suka yi wajen kwato wasu daga cikin 'yan matan.
A yanzu haka 'yan matan suna hannun rundunar sojin Najeriya.
Kafin wannan sanarwar, Gwamnatin jihar ta bayyana cewa daga cikin yan makarantar 926, guda 50 ne suka bace amma ana ci gaba da samun labarin wasu daga ciki da suka gudu.
Zamu kawo muku karin bayani da zarar mun samu.