Rahotanni dai na cewa gwamnatin jihar Adamawan ne ta hana kafa allon tallata takarar gwamnan jihar Gomben ne wato billboards, a wasu wuraren hada-hadar jama’a, lamarin da yanzu ke ci gaba da ja cece-kuce a ciki da wajen jihar.
Shi dai gwamnan jihar Gomben Ibrahim Hassan Dankwambo na cikin wadanda suka nuna sha’awarsu na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP. Kuma wannan umarnin cire allo da hotunan gwamnan na kunshe ne a cikin wata wasika da hukumar kula da birane ta Jihar wato Adamawa State Urban Planning, ta aikawa ofishin kamfen na Dankwambo.
To sai dai kuma wannan umarnin tuni ya jawo martani mai gautsi daga magoya bayan gwamnan Jihar Gomben 'yan jam’iyyar PDP,inda suke zargin da walakin goro a miya.
Alhaji Halilu Hammanjoda kusa ne a jam’iyyar PDP a Adamawa na cikin magoya bayan Dankwambo,ya ce tun farko sai da suka nemi izini tare da biyan duk kudaden da suka kamata a biya hukuma, to kuma sai ga sako daga gwamnatin jihar na cire alluna da hotunan Dankwambo.
Kawo yanzu, duk kokarin ji daga bakin shugaban hukumar raya biranen ya ci tura.Sai dai kwamishinan yada labaran jihar Adamawa, Ahmad Sajo ya bayyana dalilan daukan wannan mataki.
"Sun je sun makala hotunansa ba tare da sun tuntubi hukuma ba, basu bincika ba, allunan hotunan akwai hukuma ta raya birane da ke kula da wannan akwai kuma kudaden da ake biya. Basu gayawa kowa ba, basu biya wa'yannan kudaden ba hatta wadanda suka kafa wannan allon ma basu tuntube su ba," inji Sajo.
Haka nan kuma kwamishinan ya karyata zargin cewa gwamnatin jihar na marawa wani dan takarar PDP baya da hakan yasa aka hana kafa allon tallan Dankwambo.
Your browser doesn’t support HTML5