Cece-Ku-Ce Kan Rashin Tsaro A Arewa

kasawar gwamnati ta sa maharba sun tashi tsaye su na kare rayukan da dukiyoyin su daga hare-haren Boko Haram.

Wasu na ganin cewa kasawar gwamnati, kasawa ce ta 'yan arewan dake kan mukaman kula da tsaro

Muhawara da cece ku ce da yarfe da musanyar kalamai sun kaure akan gazawar gwamnatin Najeriya da kasawar ta wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummomin arewacin Najeriya, musamman ma yankin arewa maso gabas.

Wannan cacar baki ta barke ne bayan kiran da wasu manyan wasu yankunan Najeriya suka yi cewa a sanya cikakkiyar dokar ta baci a shiyoyin da ruwan rikici ya ciwo a Najeriya.

'Yan Najeriya da yawa, musamman ma 'yan kudanci sun dage su na cewa wasu 'yan arewacin Najeriya ne ke rike da al'amuran tsaro a gwamnatin kasar.

Wasu kuma daga arewacin kasar na ci gaba da bayyana mamakin su, da yin tambayoyin neman amsa game da yadda ake ci gaba da hallaka bayin Allah a arewa maso gabas tun shekarar dubu biyu da tara (2009).

Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa a Abuja Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko:

Your browser doesn’t support HTML5

Musanyar kalamai tsakanin Arewa da Kudu kan matsalar tsaro.-3':03"