Lamarin da wasu 'yan jihar da kuma 'yan adawa ke kukan cewa ya tsaida harkokin gwamnati.
Ko a kwanaki sai da 'yan majalisa da sauran mukarraban gwamnati suka bi gwamnan zuwa Abuja domin kai masa kasafin kudi domin ya rattaba hannu a kai.
Daga baya 'yan majalisar suka kada kuri’ar amincewa da salon gwamnatin jihar.
Batun da wasu ke ganin da walakin goro a miya.
To kawo yanzu dai ba a san ranar komawar gwamnan gida ba.
Hadimin gwamnan na harkokin yada labarai, Mr Bala Dan Abu ya bayyana wa Muryar Amurka cewa a ganinsu gwamnan yana da ikon ya gudanar da mulkin jihar a ko’ina.
Ya ce, ‘’tsaya ka ji, duk wadannan korafe-korafen basu da tushe, domin mai girma gwamna na da ikon gudanar da mulki a ko ina, kuma ba sai ya bai wa mataimakinsa mulki ba.” A cewar hadimin, sukar gwamnan kawai ake kokarin yi.
Shi kuma Ambassada Hassan Jika Ardo, tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar, wanda yanzu shi ne jakadan Najeriya a yankin Trinidad and Tobago, ya zargi 'yan majalisar dokokin jihar da zama 'yan amshin shata.
Ya ce, “ya kamata mu yaki wadannan ‘yan majalisa, yaya za a ce sun zauna gwamna ya bar jiha sama da watanni biyu, kuma babu wani abin kirki da gwamnan ya tabuka tun da ya hau mulki.”
Shi dai kakakin majalisar dokokin jihar, Joseph Albasu Kunini ya ce basu saba ma doka ba, kuma tafiyar da gwamnan yayi ba laifi bane ba.
A bangaren shari’a kuma, lauya Idris Abdullahi Jalo, wani masanin shari’a a jihar Tarabar, ya bayyana ma 'yan jarida cewa “Idan gwamna ya wuce kwanaki 21 baya nan kuma ya kasa gudanar da aikinsa, ya kamata 'yan majalisa su tabbatar cewa mataimakin gwamna ya zama mukadashin gwamna saboda kada aikin gwamnatin ya samu cikas.”
A yanzu, ‘yan siyasa da mutanen garin Taraba duk sun zuba ido domin ganin yadda wannan lamarin zai kaya.
Saurari cikakken rahoton a sauti daga bakin wakilinmu Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5