Tsohon mai tsaron gida na Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, kuma mai tsaron gida a kungiyar kwallon kafa na kasar Spain Iker Casillas ya bada sanarwar ajiye takalmansa na taka leda wa kasarsa ta haihuwa watau Spain.
Casillas mai shekaru sama da talatin da haihuwa ya fara kama wa kasar wasa tun shekara 2000 kimani shekaru goma sha shida Kenan, ya zamo kaftin din Kungiyar kwallon kafa ta Spain a 2008, ya samu nasarori da dama yayin da yake fafata wa kasar cikin nasarorin da ya samu harda cin kofin duniya na shekarar 2010.
Casillas ya ce zai daina bugawa kasar sa wasan kwallon kafa domin ya baiwa matasa masu jini ajika waje suma su gwada irin tasu bajintar domin shi girma ya kamashi. Shi dai Casillas, yanzu haka yana buga wasan ne a kungiyar kwallon kafa ta FC Porto.
Mai tsaron gida na Manchester United David de Gia, shine ya maye gurbin Casillas a kungiyar kasar Spain.
Ranar lahadi Spain da Italiya, zasu kara a gasar neman gurbin shiga cin kofin kwallon kafa ta duniya na shekarar 2018 wanda za’ayi a kasar Rasha.
Your browser doesn’t support HTML5