Rudamin da ya biyo bayan canza sheka ya janyo ma wani zababben dan Majalisar Wakilai a jihar Gombe kasa samun takardar shaidar cin zabe. Yayin da hukumar zabe (INEC) ta zo ba da takardar shaidar sai, aka ga ba sunan zababben dan Majalisar, wanda ya canza sheka daga PDP zuwa APC ba ne. Sunan wani dan APC, wanda bai ma tsaya takarar ba ne. Sanar da sunan Kamisu Mailantarki a maimakon Yaya Bauchi ke da wuya, sai mutanen da ke wurin hidimar bayar da takardar, wanda aka yi a otal din International da ke Gombe, su ka barke da ihu, sun a ta cewa, “ba ma yi!” “ ba ma yi!”
Wakilinmu na shiyyar Bauchi wanda ya aiko da rahoton, Abdulwahab Muhammad, y ace bayan da kura ta lafa, Malam Yaya Bauchi ya kira taron manema labarai inda ya bayyana cewa ko bayan da ya fita PDP ya koma APC sai da ya yi rali a garin Gombe; ya ce amma bayan komawarsa APC ba a sake taron shugabannin Majalisar Dokokin jihar Gombe ba sai bayan sama da wata guda, don haka sai ya rubuta takardar bayyana canza shekarsa ya kai wa akawun Majalisar Dokokoin jihar. Don haka ya ce zai ruga kotu kuma ya dogara da takardar shaidar barin PDP wadda ya rubuta ya kai ma ‘Ward’ Ciyaman dinsa ya rattaba hannu a kai. Da wakilinmu ya ce ai wata kotun ce ta ba da umurnin kar a saka sunansa, sai ya ce ai waccen kotun ba ta da hurumin yin hakan. Ya ce Sashi na 141 ya hana hukumar zabe ba da takardar shaidar cin zabe ga wanda bai tsaya zabe ba. To saidai Kakakin Majalisar Dokokin jihar Gombe Honorabul Inuwa Garba ya yi nuni da cewa Kamisu Mailantarki ya kai karar Yaya Bauchi Tanko cewa bai bi ka’ida ba wajen canza shekar.
Abdulwahab ya ce su kuwa gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo da Sanata Joshuwa Lidani. To saidai Sanata Danjuma Goje da Sanata Bayero Usman Nafada bas u bayyana a wurin ba.
Your browser doesn’t support HTML5