Sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Malam Mele Kyari, ya ce kawarewa da cancanta kamfanin zai duba wajen daukan ma'aikatansa ba sanayya ba.
A kwanan nan kamfanin man na Najeriya ya yi jarawabar diban ma'aikata daga duk fadin kasar wacce dubun dubatar mutane suka zana.
Malam Kyari ya kara da cewa, karkashin jagorancinsa, za a fara aikin lalubowa da tatsar albarkatun mai da suke jihohin Arewacin Najeriya nan ba da jimawa ba.
"Shugaban kasa ya ba mu ikon cewar duk inda mai yake a kasar nan mu nemo shi kuma mu fara dibar shi don sarrafawa da wadatar da kasar da mai mai rahusa ga talakawa." Inji Kyari yayin wata zantawa da ya yi Muryar Amurka.
A cewar shi, tun a ‘yan watanin baya shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ziyarci wani gari da ake kira Kwalmani da ke tsakanin jihar Gombe zuwa Bauchi, don ganin irin arzikin mai da ake da shi a yankin.
"Nan ba jimawa ba za mu sanarwa duniya adaddin yawan mai da albarkantun man da ake da su a yankin." Ya kara jaddadawa
Sannan ya ce batun iskar gas kuwa za mu ci gaba da aiki tukuru don ganin mun wadata kasar da shi cikin fara shi mai sauki.
"Sanin kowa ne cewar man fetur a fadin duniya ya yi tsada, amma hakan bai sa man fetur ya kara kudi a Najeriya ba, kusan ana ma iya cewa mai ya fi sauki a Najeriya da duk wata kasa a fadnin duniya.
A cewar Kyari, duk wanda ya taka doka, doka za a ladabtar da shi yadda doka ta tanada, yana mai cewa babu wanda zai dauki doka a hanunsa karkashin shugabancinsa.
Dangane da daukan ma'aikta a kamfanin kuwa Kyari cewa ya yi, "yanzu haka muna aikin daukar ma’aikata, za mu bai wa kowane dan kasa damar shiga cikin masu neman aiki idan Allah ya sa mutum ya cika ka’idoji babu shakka zai samu aiki ba tare da sanin wani a cikin gwamnati ba."
Ya kara da cewa, kafin karshen wa’adin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari "za’a ga duk alkawaulan da muka dauka a kasa."
Your browser doesn’t support HTML5