Lokaci yayi da masana'antar kannywood zata dinga bada dama bisa cancanta, ba sanayya ba inji Malama Hauwa Mohammad Kawo, idan har ana son masana’antar ta bukasa fiye da yadda ake zato
Malama Hauwa Mohammad ta bayyana haka ne ayayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA, Baraka Bashir, dangane da sabuwar makarantar da aka bude domin koyar da aikin jarida da harkokin fina-finan Hausa.
Ta ce makarantar zata baiwa matasa da ke sha'awar shiga harkar fina-finan sanin kaidojin da hanyoyin da zasu bi domin samun shiga harkar fim da ma irin rawar da ya dace su taka, ta kara da cewa harkar fina finai harka ce da ake samun alheri sabo da haka yakamata a samu kwararru masu gudanar da harkar.
A wasu lokutan akan samu raashin samun abinda ya dace a wasu fina-finan inda ya kamata a nuna bakin ciki ko anuna akashin haka ko a nuna ya wuce kima, ita makarantar zata magance ire-iren wadannan matsaloli.
Ta ce makarantar Filmlaps zai bada horo kashe uku , kama daga na dalibai zuwa wadanda suke cikin sana'ar fim ko jarida game da furudososi.
Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar mu da Malama Hauwa
Your browser doesn’t support HTML5