Daruruwan tsaffin mayakan kungiyar Boko Haram da mutanen da tayi garkuwa da su ne ke kan layi domin karbar abinci a garin Mozogo, dake kan iyakar Kamaru da Najeriya. Da ganinsu sun gaji kuma suna jin yunwa.
Cikin su har da Asta Hamina mai shekaru 45 a duniya, wadda sojojin kasar Kamaru suka kawo ta wannan sansani makon da ya gabata. Ta ce sun tsuntota ne a cikin dajin Sambisa, inda ‘yan Boko Haram ke da karfi a baya.
Hamina taceidan ta tuna da irin azabar da ta sha a dajin Sambisa, tana matukar tsoro da addu’ar irin hakan ba zai ‘kara faruwa a gareta ba a rayuwarta. Tace fatanta shine ta koma gida ta sake bude wani sabon babi na rayuwarta.
Amma kuma fatan na ta na komawa gida ba lalle bane ya tabbata a kwana kusa. Wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su, sun yi ikirarin cewa bayan da mayakan Boko Haram suka kai musu hari suka kamasu a kauyukansu suka tafi da su Najeriya, an tilasta musu wajen zama mayakan kungiyar, an kuma yi amfani da ‘ya ‘yansu a matsayin ‘yan kunar bakin wake.
Arouna Abba, wani shugaban al’umma a garin Mozogo, ya ce a halin yanzu basu shirya karbar wadannan mutane da aka yi garkuwa da su ba, yana cewa wasu daga cikinsu an cusa musu akidar kungiyar Boko Haram.
Arouna Abba yace da farko dai suna son gwamnatin Kamaru ta tabbatar musu da tsaro da hanyoyin kare lafiyarsu. Yace ababen rayuwa a kauyan ba zasu ishe su ba idan har suka bar wadannan mutane suka dawo. Saboda yanzu haka ‘yan kauyen na fama da matsalar karancin ruwan sha, wanda zaiyi kamari idan har suka karu.
Garin Mozogo na ‘daya daga cikin garuruwan da suka yi fama da ta’addancin Boko Haram, inda aka kone musu makarantu da kasuwanni da Majami’ada Masallatai.
Mijin Yawa Bakari, gwamnan jihar Arewa mai Nisa, yayi kira ga al’umomin yankin da cewa su hakura su karbi mutanen, ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnati zata basu tsaro.
Yace yawancin mutanen da aka kubutar din daga kungiyar Boko Haram, sun tabbatar masa da cewa basu da wata alaka da kungiyar, kuma sun shirya dawowa domin bayar da gudunmawarsu ga ci gaban kasa. Ya ce cikin mutanen dake a sansanin akwai ‘yan mata 120 da yara maza 125 dama kananan yara masu yawa wadanda suka nemi hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Dumiya da ta samar musu da makarantar marayu a kuma kara musu tsawon lokacin zama a sansanin.
Sojojin hadin gwiwa daga Kamaru da Najeriya da Chadi da Nijar, tun shekarar data gabata suke yakar mayakan Boko Haram, amma har yanzu ‘yan kungiyar na ci gaba da zama barazana a yankin.
Tashin hankalin dai ya fara ne daga Arewa maso Gabashin Najeriya shekaru takwas da suka gabata, ya kuma yi sanadiyar rayukan mutane 25,000 da kuma yin sanadiyar sama da mutane Miliyan 2 da Dubu 600 barin gidajensu.
A saurari karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5