David Cameron, Shugaban Jam'iyyar Conservative, Ya Zamo Firayim Ministan Britaniya

Firayim minista Gordon Brown yayi murabus, ya share hanyar kafa gwamnatin farko da jam'iyyar rikau ta Conservative zata shugabanta a Britaniya a cikin shekaru 13.

Firayim minista Gordon Brown na Britaniya yayi murabus, matakin da ya share hanyar kafa gwamnatin farko da jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta Conservative za ta yi ma jagoranci cikin shekaru 13 a kasar Britaniya.

Jiya talata Sarauniya Elizabeth ta nada shugaban jam'iyyar Conservative, David Cameron, a matsayin sabon firayim minista, ta kuma bukace shi da ya kafa sabuwar gwamnati.

Daga bisani, Mr. Cameron ya fadawa jama'a a kofar gidan firayim minista dake lamba 10 Titin Downing, cewa zai kafa cikakkiyar gwamnatin hadin kai da jam'iyyar Liberal Democrat, kuma shugabanta Nick Clegg, shi ne zai zamo mukaddashin firayim minista.

Har ila yau ya yaba da abinda ya kira "aiki tukuru ga jama'a na lokaci mai tsawo" da Gordon Brown yayi, amma ya ce kasar tana fuskantar "manyan matsaloli dake bukatar a takale su cikin gaggawa."

Shugaba Barack Obama na Amurka ya buga waya yana taya sabon firayim ministan murna, ya kuma gayyace shi da ya ziyarci Washington nan gaba cikin wannan shekara. Har ila yau, Mr. Obama ya aike da sakon fatar alheri ga Mr. Brown yana gode masa saboda abinda shugaban ya kira aiki abin koyi da kuma shugabanci mai karfi da ya nuna.

Murabus da Mr. Brown yayi shi ya kawo karshen mako gudan da aka yi ana cikin rudun siyasa a kasar Britaniya, a bayan da aka rasa jam'iyya guda da ta samu rinjayen da zai ba ta ikon kafa gwamnati ita kadai ba tare da yin kawance a cikin majalisar dokoki ba.

Kafin ya fita daga fadar firayim ministan dake lamba 10 Titin Downing, Mr. Brown ya ce ya so aikinsa lokacin da yake rike da mukamin, kuma a koyaushe ya kan yi kokari ne wajen kare muradun akidoji da al'ummar Britaniya. Mr. Brown zai kuma sauka daga kan kujerarsa ta majalisar dokoki.