Samun lokacin da za’a iya cajin wayar hannu, wani lokaci nada cin rai, idan aka duba rashin samun tsayuwar wutar lantarki a kasashen mu na nahiyar Afirka.
Dalilin hakane wani kamfanin fasaha na Isra’ila ya fito da fasahar da zata sharewa mutane hawaye.
Kamfanin dai zai fito da sabuwar fasaha da ake kiranta bio-organic yakuma ce za’a iya cajin waya a cikin dakikoki talatin ko kasa da haka wajen amfani da sabuwar fasahar. Amma kamfanin dai ba zai fitar abin cajin batirin kasuwa ba har sai nan da ‘yan shekaru masu zuwa.
Kamfanin dai zai shafe shekaru uku da kuma kudi dalar Amurka miliyan shida da dubu dari biyu da hamsin, domin ganin ya cimma burinsa wajen fitowa da wannan sabuwar fasaha ta cajin batirin a cikin dakikoki talatin ko kasa da haka.
Shugaban kamfanin Dr. Doron Myerdorf, yace kamfanin na baya da shekara daya wajen ganin an samu nasarar hada wannan fasaha, haka kuma ana maganar shekaru uku kafin ganin za’a iya samun batirin a kasuwa.
An kyautata tsammanin kamfanin na iya hada gwiwa da wani dalibi dake Jihar Califonia a Amurka, wanda yaci wata kyauta wajen fitowa da hanyar da za’a iya cajin batirin waya acikin dakikoki ashirin, wanda kamafanin fasaha na intel ya bashin taimakon makaranta har dalar Amurka dubu hamsin a shekarar data wuce.
Your browser doesn’t support HTML5