WASHINGTON, DC: —
Shahararriyar ‘yar wasan kwallon kafa 'yar kasar Australia Caitlin Foord, mai shekaru 25 da haihuwa, ta shirya tsaf don komawa taka leda a kungiyar Arsenal rukunin mata.
Foord, za ta bar kungiyarta ta asali Sydner FC, yanzu haka dai an kammala rattaba hannu a kwantirakinta, ana dai sa ran kocin kungiyar ta Arsenal rukunin mata Joe Montemurro, zai karbeta.
A farkon watan gobe Fabrairu, ake sa ran za ta hadu da sauran ‘yan kungiyar don fara taka leda, daga nan za su fara shirin tunkarar gasar zakaru na Olympic makonni kadan bayan isarta.