Karshenta dai kasar Burundi ta dankawa Babban sakataren MDD Ban Ki-moon wasikar bayyana kudurinta na ficewa daga cikin Kotun Laifukka ta Duniya ta I-C-C dake a birnin Hague – kuma ministan harakokin wajen Burunndi din, Alain Nyamitwe, yace “alkalamin ya bushe, ba ja da baya akan wannan kuduri.”
WASHINGTON, DC —
Kasashen Afrika da dama suna zargin wannan kotun ta duniya da cewa tunda aka kafa ta a shekarar 2002, tafi maida hankalinta ne akan kasashen na Afrika kawai.
A farkon wannan watan ne majalisar dokokin kasar Burundi ta amince da wani shirin doka na ficewarta daga kotun, sannan ko bayanta, wasu kasashen Afrika guda biyu, Afrika ta Kudu da Gambia, su ma sun bi sahun ficewa daga kotun.