Burina Na Samu Digiri Akan Harkar Fim A Amurka – Inji Adam A Adam

Mai Bada Umarni Adam A Adam

Dandalin VOA ya sami zantawa da mai bada umarni da kuma rubuta fina finai Adam A Adam, wanda akafi sani da Adam Trooper ya kuma bayyana mana yadda ya tsinci kansa a wannan harka ta fim.

Matsayin Adam Trooper a harkar fim shine marubuci, kuma manazarci, mai kuma bada umarni. Ya bayyana mana abinda ya ja hankalinsa ga wannan harka ta fim, inda yace tun yana ‘dan shekara goma sha shida akwai wani baban abokinsa wanda ke aiki a gidan talabijin na NTA, mutumin na zuwa da abin ‘daukar hoto wato kyamara mai suna M7, shine ya fara nuna musu yadda ake ‘daukar hoto da kuma aditin wato tace hotan da aka ‘dauka. Hakan ya matukar basu sha’awa ya kuma ‘dora su akan hanyar son fara sana’ar yin fina finai.

Duk da yake bai shiga makaranta ba amma taimako daga gurin mahaifin abokinsa wanda ya koya masa yadda ake sarrafa kyamara da tace hoto hakan ne ya kawo shi inda yake a yanzu. Adam ya rubuta fina finai guda talatin da shida, cikin su kuwa fim mai suna “Mai Kilago” ya sami kyauta ta fim din yafi kowanne fim siddabaru.

Burin mai Adam shine ya tafi makarantar koyar fina finai dake Amurka, domin samun digiri akan hakar fim.