Burin Duk Wani Matashi Shine Ya Zama Abun Kwatance

Al-Ameen Abubakar Ismat

Al-Ameen Abubakar Ismat, matashi da yake gudanar da karatun shi a matakin digiri na biyu a jami'ar Coventry dake kasar Burtaniya, wanda yake ganin cewar akwai hanyoyi da suka kamata matasa su bi don cin gajiyar kuruciyar su.

Matshin ya gudanar da karatun shi a matakin Firamari da Sakandire a Najeriya, wanda daga bisani ya fita kasar waje don gudanar karatunsa a matakin digirin farko har zuwa na biyu a kasar Ingila.

Haka kuma ya bayyana cewa a duk lokacin da matashi ko matashiya suka tashi tsaye wajen neman ilimi, da tunanin yadda zasu bada tasu gudunmawa wajen cigaban al'uma, lallai babu shakka zasu samu nasara.

Don cigaban wannan tattaunawar sai a biyo mu.

Your browser doesn’t support HTML5

Burin Duk Wani Matashi Shine Ya Zama Abun Kwatance 3'20"