Mahalartar taron tattalin arzikin na kasa da kasa da a keyi yanzu a Abuja sun fahimta cewa bata yiwuwa a samu bunkasar tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma idan akwai matsalar tsaro
WASHINGTON, DC —
Mahalarta taron kasa da kasa akan tattlin arziki sun fahimtu cewa habbaka tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma ba zasu yiwu ba a kowace kasa idan har ana fama da matsalar tsaro.
Haka ma da kyar yankin Afirka ya cigaba a harkokin tattalin arziki idan rashin tsaro ya yiwa nahiyar katutu. Wannan bayanin ya fito ne daga masu gabatar da jawabi da suka fito daga kasashe daban daban na duniya a wurin taron tattalin arziki na duniya dake gudana a birnin Abuja.
A wurin taron Najeriya ta nuna a zahiri cewa a shirye take tayi wani habbasa na tabbatar da tsaro a kasar tare da hadin kan kasashe daban daban musamman wadanda suka yi mata alkawari. Sabili da haka a lokacin da shugaban Najeriya yake jawabinsa ya jinjinawa kasashen nan na Afirka da Faransa da Biritaniya da China da ma kasashe daban daban da suka yi alkawarin bada gudummawa domin yaki da ta'adanci dake gudana a kasar yanzu.
Bugu da kari matsalar sace daliban Cibok sama da dari biyu ya kasance wani daratsi da kowa ke ta'allaka maganganunsa da jawabansa lamarin da ya nuna duniya gaba daya zata yiwa kungiyar Boko Haram taron dangi domin a murkusheta cikin dan karamin lokaci.
Ministan ciniki da kasuwanci na jamhuriyar Niger Malam Alma Umaru yace lallai mahalarta taron sun nuna mahimmancin tsaro akan nahiyar Afirka. Yace idan ba'a magance matsalar tsaro ba to ba zai yiwu a samu cigaban tattalin arziki a nahiyar ta Afirka. Amma yace bisa ga duk alamu an doshi hanyar warware matsalar tsaro a Najeriya ganin irin alkawuran da aka yi ma kasar da kuma matakan da aka fara dauka. Yace bayyanai sun nuna cewa Afirka a shirye take ta yaki ta'adanci tare da taimakon kasashen ketare.
A zahiri kasa bata cigaba idan babu ayyukan yi. Ba za'a samu zaman lafiya ba idan mata da matasa basu da aikin yi. Masu masana'antu ba zasu iya habaka ba su taimaka kamar yadda Aliko Dangote ya keyi.
Matsalolin talauci, cin hanci da karbar rashawa da rashin shugabanci na gari da tashe-tashen hankula kamar a Najeriya ganin yadda mutanen Afirka basu damu da matsalolinsu ba suna iya hana kasashen waje saka jari a nahiyar. Sai dai Malam Umaru yace duk wata matsala da ake fuskanta a Afirka kasashen waje sun fuskanceta da can baya. Amma idan mutane suka amince da kasarsu suka dauki yanayin da za'a yadda dasu masu saka jari zasu shigo su saka jari.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5