Bunkasa Ilimi: Jami’ar Afirka Da Ke Sudan Za ta Hada Kai Da Jami’ar Maiduguri da ke Najeriya

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan makaranta a Maiduguri

A cigaba da fadi-tashin da ake yi na inganta ilimi a Afirka, wasu jami'o'i masu matukar tarihi a Sudan da Najeriya sun hada kai wajen yada ilimi a nahiyar. Ganin wanin yadda wannan yinkurin ke samun goyon bayan wani attajiri mai sha'awar iza ilimi, mutane da dama za su kyautata zaton kwalliya za ta biya kudin sabulu.

A wani yinkuri na ciyar da ilimi gaba a Afirka, Jami’ar Kasa da Kasa ta Afirka da ke Sudan da Jami’ar Maiduguri da ke Najeriya sun yanke shawarar hada kai a fannoni da dama. Tawagar Jami’ar Kasa da Kasar karkashin jagorancin Furfesa Mahmud Abdulrahman El-Sheikh ya ce sun zo Najeriya ne saboda a kammala tabbatar da yarjajjeniyar da aka cimma tsakanin jami’o’in biyu tun a watan Agusta.

Furfesa Mahmud ya ce an cimma yarjajjeniyar ce a fannonin da dama da su ka hada da musayar dalibai da malamai da nau’ukan tarurrukan bunkasa ilimi da bincike mai zurfi da fannin likita da dai sauransu. Ya ce jami’o’in za su hada kai sosai a wadannan fannonin don bukasa ilimi da kuma amfanar jami’o;in.

Shugaban Gidauniyar Indimi, Alhaji Muhammadu Indimi wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wajen tabbatar da wannan ‘yarjajjeniyar, wanda kuma shi ke wakiltar Afirka a Kwamitin Amintattu na jami’ar ta kasa da kasa da ke Sudan, ya ce kasashen duniya sun kafa jami’ar ce saboda su bunkasa ilimi a duniya. Ya ce jami’o’in biyu sun kafa kwamitin mutane shida-shida don cimma wannan burin.

Ga wakilinmu a Abuja, Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Bunkasa Ilimi: Jami’ar Afirka Da Ke Sudan Za ta Hada Kai Da Jami’ar Maiduguri da ke Najeriya