Galibin Duniya rtayi Bukukuwan Shigar Sabuwar Shekara 2017.

Sabuwar shekara ta 2017.

Kasashen New Zealand, da Australia da Rasha suna jerin kasashen da suka fara ganin sabuwar shekara.

Galibin duniya tayi bukukuwan shigar sabuwar shekara 2017, tareda wasannin wuta, da yin liyafa,da dai wasu bukukuwa, duk da cewa wasu suna bakinciki da nuna alhini idan suka duba harkokin siyasa da wasu fannonin rayuwa a shekarar da ta shude mai cike da rigingimu.

Kasashen New Zealand, da tsibirai da suke yankin Paicific, da Australia, da Rasha suna cikin jerin kasashen duniya da suka fara yin bikin shiga sabuwar shekara ta 2017.

Daya daga cikin manyan bukukuwan shigowar sabuwar shekara shine wasan wuta da ake yi duk shekara a birnin Sydney na Australia, inda mutane fiyeda milyan daya suka hallara suka yi cicirindoa gabar ruwa domin su kalli wasannain wutan da aka yi da zummar karrama mawakin nan David Bowie, da kuma dan wasan fina-finai Gene Wilder, wadanda suka mutu a bara.

Kasashen duniya da dama suna maida hankali ne kan tsaro, inda suke tsammanin jama'a masu dumbin yawa zasu fito domin bukukuwan murnar shiga sabuwar shekara.

Wani hari da aka kai a wani Club a Istanbul na Turkjiyya, ya birkita bikin shiga sabuwar shekarar, mutane 35 aka kashe a harin.

Hukumomi a biranen duniya masu yawa sun kara dauakr karin matakn tsaro, biyo bayan harin da aka kai a Jamus da wata motar dakon kaya, harin da ya halaka mutane 12, da kuma dai wasu hare hare da aka kai a bara.

A Dubai dubun dubatan mutane ne suka kalli wasan wuta da aka kaddamar a benenen nan mafi girma a duniya da ake kira Burj khalifa.

An tsaida masu gadi ko wani mita 50, kuma an dakila sashen masu tafiya da kafa domin tabbatar da hanyoyi suna bude domin motocin agajin gaggawa su sami sukunin tafiya.

A Moscow shugaban Rasha Vladimir Putin, yace "ko wani mutum yana iya zama dan siddabaru a dare mai kamada irin wannan" ta wajen mutunta dangi, ko abokan aiki,ko aminai, da mabukata.

Shugaban Faransa Francois Hollande yayi amfani d a kjawabinsa wajen yin gargadi gameda karin mutane masu zama 'yan kishin kasa.
A fadar Vatican, Papa Roma Francis yayi kira ga mabiya darikar katholika su taimakawa matsa su sami abin yi tsakanin al'uma.

Shugaban Amurka Barack Obama a jawabinsa na mako mako a ranar ko wace Asdabar, yayi amfani da damar wajen duba shekarar 2016, da kuma shekaru 8 da yayi yana shugabancin Amurka. Ya kare jawabinsa nasa da cewa "daga Obama da iyalinsa zuwa ga naka iyalin, barka da sabuwar shekara 2107 ,Allah yayi mata albarka.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya aike da gaisuwa domin sabon shekara ta Twitter yana cewa "Barka da sabuwar shekara gareku duka, harda makiya na masu yawa, da kuma wadanda suka yake ni kuma suka yi mummunar faduwa har ma basu san abunda zasu yi ba. Ga kauna.