Yayin da ake harmar bukukuwan Sallah, hukumomi a Najeriya sun ce suna kan daukar matakan da su ka dace don kare ‘yan gudun hijira musamman ma wadanda ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijiran daban-daban.
Wakilinmu a shiyyar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ce tuni ma aka kara yawan sojoji da ‘yansanda a sansanonin. Ya ruwaito babban jami’in hukumar NEMA mai kula da sansanomnin ‘yangudun hijira da ke jahar Adamawa, Alhaji Sa’ad Bello na cewa hatta yadda ake saka ido da kuma bincike ya karu a harabar sansanonin. Y ace baya ga sojoji da ‘yansandan da aka kara, an kuma kara yawan ‘yan sintirin sa-kai.
Alhaji Sa’ad y ace baya ga kara ingancin matakan tsaro, an kuma hada kai tsakanin hukumar NEMA ta SEMA ta jahar wajen samar da kayan more rayuwa ma ‘yan gudun hijirar saboda su yi bukukuwa cikin anashuwa da kwanciyar hankali. Ibrahim y ace wasu jiga-jigan jahar Borno sun je don yin bukukuwan Sallar da su saboda karfafa masu gwiwa.
Your browser doesn’t support HTML5