Tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama da yake jawabi a wajen taron bukin ya ce, “Al'ummar Hausawa sun ba da gudummawa kwarai wajen ci gaban kasarmu tun daga lokacin da aka fara shiri har zuwa lokacin haihuwar kasarmu Ghana. Hausawa sun taka rawar gani mara misaltuwa a yakin neman yancin kasar Ghana”.
Ya kara da cewa, dakarun soji sun yi amfani da harshen Hausa kwarai wajen maci a lokacin Gold Coast, kafin Ghana ta samu ‘yancin kai.
Bukin Ranar Hausa ta Duniya na burin hada kan al’ummar Hausawa a duk inda suke a fadin duniya tare da yada al’adun gargajiyarsu. Bukin wannan rana a birnin Accra ya tabbatar da hakan, domin an baje kolin al’adun Malam Bahaushe inda ‘yan tauri, da masu rawar koroso, da mahaya dawakai suka kayatar da filin taron.
Wasu da suka halarci wajen da Muryar Amurka ta ji ra’ayinsu game da bukin wannan shekarar, kamar sarkin Anya kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar sarakunan zangon Ghana, Alhaji Jibril Sissy, da shugaban kungiyar hadin kan Hausawan duniya, Mohammed A. da magajiyar sarkin Hausawan Nima, Hajiya Azumi Ibrahim sun bayyana farin cikinsu da bukin wannan shekarar, musamman jawabin da tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama, ya yi matukar kayatar da su.
Jama'a dai sun bayyana farin cikinsu da bukin wannan shekarar, musamman jawabin da tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama, ya yi matukar kayatar da su.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako:
Your browser doesn’t support HTML5