Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa Amurka ta kai makura a Afghanistan, a daidai lokacin da Amurkawa ke kawo karshen yakin da su ke yi a wurin zuwa karshen wannan shekarar.
WASHINGTON, DC —
A wani bangare na shagulgulan Ranar Tuna 'Yan Mazan Jiya da aka yi jiya Litini, Mr. Obama ya jinjina ma wadanda su ka rasa rayukansu a Afghanistan, da kuma dukkannin wadanda su ka mutu a yake-yaken da Amurka ta yi. Ranar Lahadi Mr. Obama ya kai ziyarar bazata ga sojojin Amurka maza da mata da ke Afghanistan, inda kusan dukkannin sojojin Amurka ke shirin ficewa zuwa karshen 2014.
A nan gida kuma a jiya Litini, ya ajiye furanni a kabarin wani sojin Amurka da ba san shi ba a Makabartar Kasa Ta Arlington da ke kusa da birnin Washington. Ya ce da dama daga cikin mu ba za su taba sanin irin jajircewa da sadaukarwar da iyaye da 'yan'uwan wadanda su ka rasa rayukansu su ka bar 'yan'yansu da matansu da dangoginsu a wuraren yaki ba.
An yi bukukuwan Tuna 'Yan Mazan Jiya din ne da dogayen fareti da kada tutoci da yin shiri tsit, da kuma zuwa wuraren shakatawa.