Sanata Bukar Abba Ibrahim na jahar Yobe,ya kawo karshen takaddamar siyasa tsakanin sa da gwamna Ibrahim Gaidam wajen janye muradin sa na tsayawa takarar tazarce a kujerar Sanata, inda ya kauce don ba wa gwamnan damar takarar, kasancewar sun hada mazaba daya.
Sanata Ibrahim wanda ya zama gwamnan Yobe a lokuta 3, ya daga hannun gwamna Ibrahim Gaidam a wani taro a Abuja don neman ya maye gurbin sa a majalisar dattawa, bayan ya zauna a majalisar a wa’adi 3.Kazalika Sanatan da ya ce ya haura shekaru 70 a duniya, ya daga hannun sakataren APC Mai Mala Buni don neman takarar gwamnan Yobe ba hamaiya a jam’iyyar.
Gwamna Ibrahim Gaidam ya ce dama an kanbama batun ba sa jituwa da Sanata Bukar Ibrahim ne, amma bayan tattaunawa yanzu Bukar ya zama kakan siyasar jihar inda shi kuma ya ce ya zama uban siyasar jihar da ke farfadowa daga illar Boko Haram.
Saurari Rahoton Nasiru Elhikaya domin jin cikakken bayani...
Your browser doesn’t support HTML5