Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin yaki da akidar bauta da kuma cinikin bayi musamman ma kamar yadda yak e faruwa ko kuma ya faru a kasar Libiya.
Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke halartar taron Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka a kasar Ivory Coast. Ana tattaunawa ne a taron a kan batutuwa da dama, ciki har da batutuwan matasa da na al’umma baki daya. Hasali ma taken taron shi ne Tallawa Matasa Domin Cigaba Mai Dorewa a Duniya.
Daraktan yada labarai a Fadar Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya bayyana ma wakilin Sashin Hausa a Fadar Shugaban Najeriya Umar Faruk Musa cewa baya ga Shugaba Buhari akwai kuma wasu magabata da dama da wannan mummunan al’amari ya dame su. Ya ce kodayake kasar ta Libiya ta yi ta kokarin kare kanta, to amma Shugaba Buhari na da cikakken bayanin irin yadda aka yi ta wulakanta ‘yan Najeriya a kasar ta Libiya.
Ya ce ‘yan Najeriya da Shugaba Buhari ya sa aka dawo da su daga Libiya da kuma wadanda su ka kama hanyar Turai bayan sun bar kasar ta Libiya a yanzu sun kai dubu biyar kuma ana cigaba da dawo da sauran. To amma ya amsa cewa daga cikin abubuwan da ke sa a fita zuwa wasu kasashen har da kwadayi da kuma matsin rayuwa. Ya ce babbar mafita it ace da gwamnati da duk wani mai ruwa da tsaki su hada kai wajen warware wannan matsalar.
Your browser doesn’t support HTML5