Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi tir da harin da Boko Haram ta kai jiya Asabar kan wani jirgin agaji na Majalisar Dinkin Duniya a arewa maso gabashin kasar.
Ya mayar da martani kan harin ne a cikin wata sanarwar da fadarsa ta fitar wacce ke dauke da sa hannun mai magana da yawun fadar Malam Garba Shehu.
"Ina son in sanar da 'yan Najeriya, da ma duniya gabadaya cewa zamu dauki mataki kan wannan harin na Boko Haram wanda ya lakume rayukan mutum 2, ciki harda dan shekara 5."
Shugaban ya kuma jadadda cewa tsaron 'yan kasar waje da kuma 'yan Najeriya, shi ne babban abinda gwamnatinsa ke mayar da hankali kai.
A karshe ya bayyana muhimmancin duk wasu kungiyoyin agaji a yankin su hada kai da rundunar soji domin tsara duk wasu tafiye-tafiye da zasu yi.