A yau Litinin, Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja, babban birnin kasar.
Wannan ganawar tasu na zuwa ne a lokacin da matsalar satar mutane da kuma hare-haren 'yan bindiga ke ci gaba da karuwa a wasu sassan kasar musamman ma a arewaci.
Ko da yake, Buratai bai fadi takamaiman abin da suka tattauna da Shugaba Buhari ba amma ya bayan ganawar ya fadawa manema labarai cewa, hukumomin tsaro na bukatar taimakon dukannin 'yan Najeriya domin a iya shawo kan matsalolin.
Jaridar Punch ta ruwaito babban hafsan yana cewa, "kashi 90 na maharan 'yan Najeriya ne kuma suna zaune a cikinmu," kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A kwanakin baya ma shugaban na Najeriya ya gana da shugabannin tsaro inda ya amarce su da su kara sa himma wajen kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar kasar.
Cikin watan da ya gabata, shi ma Buratai ya hadu da wasu sojoji a wani taron da suka yi, inda ya ce a ganinsa sojojin "ba sa iya kokarinsu wajen shawo kan matsalolin tsaro."
Ko a safiyar jiya Lahadi sai da 'yan bindiga suka kai wani hari a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 3.