A wannan takarda da mai magana da yawun sa ya aikewa manema labarai a kasar na cewa, Shugaba Buhari ya ce ana ta kokarin tada hankali a cikin Jamiyyar ne a gabanin babban taron ta na kasa a ranar 26 ga wannan wata na Maris.
Buhari ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa Shugabanni da 'ya'yan Jamiyyar gargadi da su guji tada zaune tsaye da yin kaurin suna yayin da ya kamata a mayar da hankali kan wanda zai fito a matsayin dan takarar shugaban kasa a Jamiyyar, domin shi ne muhimmin abu ga kasar a yanzu, ba batun shugabanicn Jamiyya ba.
Har ila yau, wannan takarda da Buhari ya bada umurnin a aikawa manema labarai na cewa jigajigan Jamiyyar APC su sa hankalin su a kan abubuwan da zasu amfani Jamiyyar da talakawan kasar, ba cece-kuce a kan mukamai ba. Akan haka tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Bauchi Shuaibu Abubakar Ismail, ya yi tsokaci a kan wannan batun yana mai cewa suna karfafa wannan magana
Tsohon Sanata daga jihar Yobe kuma jigo a Jamiyyar APC Alkali Abdulkadir Jajere ya ce lallai wanan jan kunne da Buhari ya yi, shi ne daidai.
A nashi nazarin Kwararre a harkokin Siyasar Kasa da Kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk yana ganin irin wannan mataki na tsawatar wa ne ya kamata Shugaba Buhari ya rika yi saboda a kwato Jamiyyar daga rugujewa.
Sakon Buhari ya zo ne a daidai lokacin da ake yada jita jita cewa Mataimakin Shugaban Kwamitin rikon kwarya kuma Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya karbe Kujerar shugaban Kwamitin kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Wasu jijajigan jamiyyar na cewa, ‘yan bani na iya da masu son kawo wa jamiyyar bakin jini ne suke dagula al'amura a Jamiyyar
Ga Medina Dauda da rahoto daga Abuja Najeriya:
Your browser doesn’t support HTML5