Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa jami'an tsaro umurnin so zakulo maharan da suka kashe mutane 19 a karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato a cewar jaridun kasar.
A wata sanarwa da shugaban ya fitar mai dauke da sa hannun mai bashi shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, shugaba Buhari ya nuna alhinisa musamman kan kisan mata da yara kanana da aka yi kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Jaridar Daily Trust ma da ake bugawa a birnin Abuja, ta ruwaito sanarwar ta Malam Garba Shehu, inda shugaba Buhari ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci ta da tarzoma ba.
Wasu mahara ne suka far ma kauyen Ancha da ke karamar hukumar Bassa a daren Juma'a suka kashe mutanen ciki har da yara kanana da mata.
‘Yan sandan dai na zaton cewa kila harin na ramuwar gayya ne bayan da aka kashe wani yaron Fulani a kwanakin baya, wanda jami’an tsaro suka damke mutane biyar suke tuhumarsu kan kisan
Tuni dai gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya yi Allah wadai da harin wanda ya kwatanta a matsayin yunkurin ruguza zaman lafiyan da jihar ke cin gajiya, bayan fama da jihar ta yi da rikice-rikicen da ke da nasaba da kabilanci da addini.
Saurari rahoton Zainab Babaji kan ainihin harin da aka kai Filato:
Your browser doesn’t support HTML5