Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya taya tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Wata sanarwa ce dauke da sa hannun mai bai wa shugaban Najeriya shawara a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, wacce Muryar Amurka ta samu, ta bayyana cewa shugaba Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekara 82 a duniya.
“Duk da banbance-banbancen siyasa da muke da su da Obasanjo, ina mai ci gaba da kallonsa a matsayin mutum mai matukar kima, saboda irin gudunmuwar da ya bayar wajen ciyar da Najeriya gaba ta wuce banbance-banbancen da ke tsakaninmu.” Sanarwar ta nuna.
Buhari ya kara da cewa, “Cif Obasanjo, ya nuna halayen da za a yi koyi da shi sannan ya kwadaitar da na kasa da shi da irin dabarun iya shugabanci da yake da su.”
A cewar Buhari, mika mulki da Obasanjo ya yi ga gwamnatin farar hula a watan Oktoban shekarar 1979, na daga cikin irin gudunmuwar da ya bayar wajen ci gaban kasa.
“Yayin da yake bikin cika shekara 82, ina mai yi wa Cif Obasanjo fatan samun karin lafiya.” Inji Buhari.