Shugaban Najeriya ya sallami shugaban hukumar da ke yaki da masu yin tu'annati ga tattalin arzikin kasa Ibrahim Lamorde.
WASHINGTON D.C. —
Rahotanni daga Najeriya na cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu tu’annati ga tattalin arzikin kasa wato Ibrahim Lamorde.
Wata sanarwa da ta fito da sa hanun mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin 'yan jarida, Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari ya amince da nadin Mr Ibrahim Mustafa Magu a matsayin shugaban hukumar na wucin gadi.
A da Mr. Magu ya kasance mataimakin kwamishinan 'yan sanda ne, shi zai canji Lamorde wanda ya tafi hutun barin aiki yayin da wa'adin kammala aikinsa (Lamorde) ke karatowa a watan Fabrairu mai zuwa.