Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya halarci wani gangamin yakin neman zabe a garin Bauchi ranar Alhamis. Cikin wadanda suka rufa masa baya har da gwamnonin APC shida, da ministoci da 'yan majalisun tarayya, da kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, da dai sauransu.
A jawabin da shugaban ya yi, ya jaddada anniyarsa ta ci gaba da yaki da wadanda ya kira azzaluman kasa da suke sace dukiyar talakawa. Ya fada cewa aikin da ya keyi yana yi ne domin talakawan kasar da kuma kasar. Ya ce ba zasu yadda a cuci talakawa ba. Shugaba Buhari yace abun dake gabansu shi ne kyautata kasa, kayautata tsaro, da tattalin arziki da rayuwar al'umma. Cikin addu'ar da ya yi yana fatan Allah ya kara tona asirin munafukan kasar.
A jawabin da ya yi shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole, ya ce ba zasu yadda mara sa gaskiya su ci gaba da kasancewa a jam'iyyarsu ba. Duk wadanda suke son a rika watanda da kudin jama'a su tafi.
Shi ma gwamnan jihar Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar, ya ce lokacin rabuwa da baragurbin mutane ya yi. Ya ci gaba da cewa lokacin raba gari da wadanda ya kira "wake-wake" ya wuce. Ya godewa Allah da ya nuna masu wadanda ya kira "wake-waken" tun farko kafin a yi nisa. Gwamna Abdullahi yace babu wani mahaluki a kasar da zai fito ya ce Shugaba Buhari bai iya tafiyar da tattalin arziki ba.
A saurari rahoton Abdulwahab Muhammadu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5