Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen tarbar watan Ramadan, watan da Musulmai ke tsawaita ibada.
A cikin wata sanawar da Buhari ya fitar ta hannun Kakakinsa, Malam Garba Shehu, Shugaban ya aike wa 'yan Najeriya da ma Musulmi a duk fadin duniya, sakon cewa wannan lokaci ne da ke ba da dama ta musamman na ''jin yunwar da talakawa ke fama da ita''.
Shugaban ya shawarci attajirai Musulmi da su guji almubazzaranci yayin da wasu ke fama da yunwa da fatara, inda ya bukaci da su kula da makwabtansu, talakawa da marasa galihu.
Ya kuma yi kira da a yi addu’o’in samun zaman lafiya a kasar nan da ma wajenta, da kuma samun lafiya da zaman lafiya a fadin duniya.
Ya kara da yin fatan kammala azumin kwanaki 30 cikin nasara.