Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Hana Ba-haya A Fili

Injiniya Suleiman Adamu, Ministan Ruwan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akan wata doka da ta hana yin ba-haya ko fitsari a bainar jama’a da kuma wasu al'amuran da suka shafi hakan.

An yi wa dokar lakabi da “kawar da matsalar ba-haya a fili a Najeriya nan da shekarar 2025."

Ministan ma'aikatar Ruwa na Najeriya, Inginiya Suleiman Adamu, ya bayyana cewar an yi wannan dokar ne don tabbatar da an samar da muhalli da ruwan sha masu tsafta a kasar baki daya.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fuskantar matsalar ba-haya ko fitsari a fili. lamarin da kan haifar da illoli ga lafiyar al’ummah.

Indiya ita ce kasar da ta fi kowacce fuskantar wannan matsalar a duniya, amma ta dauki wasu matakai na kawo karshen hakan.

A yanzu hukumomin a Najeriya su ma sun dukufa wajen ganin an tsaftace ko ina.

Dokar dai ba tana nufin idan aka samu mutum da laifin yin ba-haya a bainar jama’a za’a hukunta shi ba ne, ana so jama’ su dauki dabi’ar tsaftace muhallansu da kansu ba tare da wani ya tsawata masu ba.

Ministan ya kara da cewar, an umurci ma’aikatun gwamnati da su samar da wadattattu da tsaftatattun makewayi a duk ofisoshinsu, kana gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi ma su bi sahu.

Akwai bukatar jama’a su ma su samar da matsugunnai a cikin kasuwanni da tashoshin motoci don samar da aikin yi da kuma karin kudaden shiga ga kasa.