Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya mayar da martani ga labaran da ake ta yadawa cewa ya mutu kuma an maye gurbinsa da wani 'Buhari na bogi' da aka samo daga kasar Sudan.
A jiya Lahadi shugaban na Najeriya, ya musanta rahotanni da ke yawo a kafafen internet, a lokacin yana tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar Poland.
Buhari ya je kasar ta Poland ne domin halartar taron da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kan sauyin yanayi a birnin Katowice.
“Ina mai tabbatar muku cewa, ni ne (Buhari) na asali, a kwanan nan ma zan yi bikin cika shekaru 76 da haihuwa kuma zan ci gaba da kasancewa da karfina.” In ji shugaban na Najeriya.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, ta nuna cewa, Buhari ya ce, a lokacin da ya yi rashin lafiya, wasu mutane sun yi ta mai fatan mutuwa.
“Wasu ma har sun fara tuntubar mataimakina (Osinbajo) domin ya dauke su a matsayin mataimakin shugaban kasa, saboda suna tunanin na mutu.”
Tun a shekarar 2017, aka yi ta yamadidi kan lafiyar Buhari a lokacin da ya je London neman magani kan wata cuta da ba a bayyana ba.