A yau Lahadi 19 ga Yulin 2015 ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara ziyarar aiki ta kwana 4 zuwa birnin Washington a nan Amurka don ganawa da Shugaban Barack Obama.
WASHINGTON D.C —
Ana kyautata zaton maganar magance matsalar Boko Haram ce babbar hancin tufkar da ake son kamawa a ziyarar tasa. Amurka na bukatar taimakawa Najeriya a kokarin yakar Boko Haram.
Wanda suka matsa tun bayan kafuwar sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari awatan Mayun da ya wuce. Wannan ziyara ce ta farko tun bayan lashe zaben Buhari a watan Maris da ya shude.
Akwai yiwuwar tattaunawa game da garambawul din siyasa da tattalin arzikin kasar don kawo karshen matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya. Ziyarar dai ta tsawon kwanaki hudu ce.