Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gwamnoni guda takwas karkashin jagorancin gwamnan Zamfara, domin neman hanyar warware matsalolin da suka shafi zabukan fitar da ‘yan takara a jam’iyyar APC.
WASHINGTON D.C. —
Ganawar ta mayar da hankali ne ga matsalolin da jam’iyyar APC ke fuskanta a jihohi, ganin yadda ake ta fama da rikice-rikice sanadiyar zabukan fitar da ‘yan takara a Najeriya.
Lamarin dake haddasa wasu manya da kananan ‘yan jam’iyyar APC ke sauya sheka zuwa wata jam’iyya ta daban. Hakan yasa shugaban kasa ya zauna da gwamnonin jihohin da suka hada da Ogun da Imo da Nija da Nasarawa da Ondo da kuma Zamfara, domin neman hanyoyin da za a warware matsalar.
Gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya shaidawa Muryar Amurka cewa ganawar na da muhimmanci gaske, ganin irin kalubalen da wasu gwamnoni ke fuskanta a jihohinsu ciki har da jiharsa ta Zamfara.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5