Shugaban najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda za su wakilci kasar a musabakar Alkur’ani Mai Tsarki na duniya, wanda za a yi a kasar Saudiyya a cikin wannan shekarar, da su nuna abin koyi. Shugaba Buhari ya mika wannan bukatar ce a sakonsa na rufe taron musabakar Alkur’ani na kasa da aka gudanar a garin Gombe a jiya Lahadi.
Da yake gabatar da jawabin shugaba Muhammadu Buhari, ministan muhalli a Najeriya Sulaiman Hassan Zarma ya fara ne da mika godiya wa ALLAH subuhanahu wata’ala, sannan yace a yayin da nake mika sakon taya murna ga dukkan wadanda suka fafata a musabakar, ina kira gare ku da ku tabbatar kun yi koyi da koyarwan addinin musulunci na hadin kai a tsakanin dukkan 'yan adam da kuma kyakkyawan dabi’a.
A nasa jawabin shugaban jami’ar Usman Dan fodiyo da ke Sakkwato farfesa Abdullahi Abdul Zuru ya yi bayanin makasudin shirya musabakar, da cewa hanya ce ta kulla abota a tsakanin 'yan kasa.
Ga dai wakilinmu a shiyyar Bauci Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5