Yayin da Najeriya ke fama da matsalar tattalin arziki al’amarin da ake alakanta shi da wawurar kudin da wasu ‘yan Najeriya su ka yi su ka boye a kasashen waje, Shugaan Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga kasashen Turai da Amurka da su taimaka su yi amfani da tasirinmu wajen ganin an maido da wadannan dinbin kudade.
Shugaba Buhari, wanda ya je birnin Paris na kasar Faransa don halartar taron zagayowar tunawa da yarjajjeniyar Armistice wadda ta tabbatar da kawo karshen yakin duniya na daya, ya gaya ma al’ummar Najeriya mazauna kasar Faransa cewa da dana bin da kasar ke da shi a halin yanzu ya ke lallabawa alhalin kuwa ga dinbin dukiyar Najeriya wasu mutane ‘yan kalilan sun boye a kasashen waje.
A wata takardar bayani, wadda Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin jarida Femi Adesina ya rattaba wa hannu, Shugaba Buhari ya tabbatar ma ‘yan Najeriya din cewa duk da wannan matsala ta rashin kudi, gwamnatin Najeriya za ta cigaba da mai da hankali kan bangaren ilimi, hanyoyi, lantarki, da kuma sauran ayyuka na gina kasa.
Wani mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum a Najeriya mai suna Aminu Sule na kungiyar Network for Justice ya ce Buhari ya yi daidai, kuma ya kamata a bi duk wata hanyar kwato wadannan kudaden muddun ba ta saba ma doka ba.
Ga dai tsakacin Malam Aminu Sule kan wannan batun. Na fara da tambayarsa yadda ya ke ganin kiran da Shugaba Buhari ya yi cewa duniya ta taimaka a dawo da wannan kudin, sai ya ce:
Your browser doesn’t support HTML5