Buhari Na Neman Majalisa Ta Ba Shi Izinin Ciwo Bashin Dala Biliyan 5

Shugaba Mohammadu Buhari na Najeriya ya bukaci Majalisar kasa ta ba shi izinin ya kara ciwo bashin kudi dalar Amurka sama da biliyan 5 da za a yi amfani da su wajen cike gibin kasafin kudin bana.

Wasikar da ke dauke da wannan bukata ta zo ne a daidai lokacin da Majalisar ke bitar kundin gyararren kasafin kudin na bana wanda an riga an kai rabin shekara ana amfani da shi.

Amma kuma ya zama dole a rage kasafin a sakamakon karyewar farashin gangar danyen man fetir a kasuwar duniya saboda cutar coronavirus.

Kafin yanzu, an gina kasafin kan kiyasin dalar Amurka 57 amma yanzu an rage shi zuwa dalar Amurka 25.

Sai dai Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba ya ce akwai abin dubawa akan wannan kasafi da aka gyara domin a ganinsa, an ce za a samu kudin shiga Naira triliyan 5.56.

Saboda haka, yana ganin ya za a ciwo bashin triliyan 4.9, inda ya yi ikrarin cewa masu tsara kasafin na kasa suna da matsala domin shekara ta kai tsakiya, saboda haka bai ga yadda wannan kasafin kudin zai yi wu ba.

Amma ga Sanata Adamu Mohammed Bulkachuwa, Majalisa za ta hanzarta yin aiki akan gyararren kasafin saboda a ci gaba da aiki da shi har zuwa karshen wannan shekara da muke ciki abinda ke nufin cewa za a iya aiwatar da kasafin kamar yadda ya kamata.

A baya bayan nan ma Majalisar ta amince wa Shugaban kasa ya karbo wasu basussuka har Naira biliyan 850 wanda aka ce za a karbo rabi a cikin gida rabi kuma daga waje.

Ga karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari Na Neman Majalisa Ta Ba Shi Iznin Ciwo Bashin Dala Biliyan 5