Buhari Na Kan Gaba Zuwa Yanzu a Zaben Shugaban Kasa

  • Ibrahim Garba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yayin da ake cigaba da tattara sakamakon zaben Shugaban kasar Najeriya, zuwa yanzu Shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, ya sha gaban Alhaji Atiku Abubakar, babban mai kalubalantarsa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Sakamako na farko-farko a zaben Shugaban kasar Najeriya, na nuna cewa Shugaba mai ci Muhammadu Buhari ga kan gaba, to amma babbar jam’iyyar adawa ta yi watsi da sakamakon, da cewa mara sahihanci ne kuma ba abin amincewa ba ne.

Hukumar Zaben Najeriya Mai Zaman Kanta (INEC), jiya Litini, ta bayyana cewa Buhari ya ci zabe a jahohi a kalla shida, a yayin da shi kuma babban mai kalubalantarsa Atiku Abubaka ya ci na babban Birnin Tarayya Abuja.

Ciyaman din jam’iyyar PDP ta su Atiku, Uche Secondus, ya ce jam’iyyarsu ta gano wasu “magudi” da aka yi a jahar Nasarawa da kuma birnin Tarayya Abuja.

Da ya ke magana a wani taron manema labarai a Abujan, Secondus ya yi zargin cewa gwamnatin Buhari ta hada baki da hukumar zabe ta INEC wajen yin cogen sakamakon runfunan zabe a fadin kasar. Secondus ya ce PDP na da abin da ya kira “sakamako na ainihi” daga runfunan zabe na fadin kasar.

An gudanar da zabe ranar Asabar a dukkannin jahohi 36 da kuma birnin taryyar Najeriya, Abuja, ko da yake hukumar zabe ta INEC ta dage zabe a wasu wuraren da abin ya zo da tangarda.