Buhari Na Iya Sake Gabatar Da Sunan Ibrahim Magu - Ndume

NIGERIA-POLITICS

Bayan da Majalisar Dattawan Najeriya ta ki amince ta tabbatar wa da mukaddashin shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu mukaminsa, shugaba Buhari na iya sake gabatar da sunan sa ga majalisar, a cewar shugaban marasa rinjaye, Sanata Muhammad Ali Ndume.

Ba yau ba ne majalisar dattawan Najeriya take kin amincewa da wasu da aka gabatar gabanta domin a ba su mukamai saboda a can baya an gabatar da wani sau shida kafin a tabbatar masa da mukamin da shugaban kasa na wancan lokacin ya nadashi.

Matakin da majalisar ta dauka na kin tantance Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC ya zo ma Sanata Ali Ndume da takaici inda ya ce su 'yan majalisa wakilai ne na jama'a saboda haka duk abun da za su yi ya kasance abun da jama'a suke so ne.

A cewarsa, a kan Ibrahim Magu, Majalisar Dattawa ba ta yi dattaku ba saboda abun da ta yi ba shi ne mutanen da suka zabe su suke so ba, ko da yake ya amince cewa haka dimokradiya ta gada..

Sanata Ali Ndume ya ce bai kamata akai ga hakan ba idan aka yi la'akari da cewa jam'iyyarsu ta APC ta na da sanatoci 65 cikin 109.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari Na Iya Sake Gabatar Da Sunan Ibrahim Magu - Ndume- 13' 20"