Buhari Da Shugabannin Afurka Biyar Sun Kaddamar Da Matatar Man Dangote

ALIKO DANGOTE

Ita dai wannan katafariyar matatar man fetur da ke wajen birnin Lagos mallakar kanfanin Dangote, wanda shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ya kaddamar, kamar yadda shugaban kanfanin na Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi bayani, shi ne mafi girma a nahiyar Afurka.

An gina ne domin sarrafa gangunan mai fiye da 650,000 a duk rana wanda aka kashe dala na gugar dala, har biliyan 20 wajen ginawa.

Don haka Alhaji Aliko Dangote ya ce a lokacin da matatar man fetur din za ta fara aiki a tsakanin watannin Yuli zuwa Agusta za ta taimaka wajen samar da man fetur a cikin gida da kuma kasashen Afurka da ma duniya baki daya.

A jawabinsa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya daga wa kanfanin na Dangote tuta bisa jajircewa wajen gina wannan katafariyar matatar man fetur irinsa na farko a Afurka.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta bai wa yan kasuwa damar kafawa da mallakar kanfanoni masu zaman kansu domin samar da aikin yi da kuma kawo karshen asarar da gwamnati ke yi wajen tafiyar da wasu ma'aikatunta.

Don haka ya yaba wa Alhaji Aliko Dangote kan wannan aiki na gina matatar mai da za ta rage irin kudin da Najeriya ke kashewa wajen bada tallafin man fetur.

Shi ma a bangarensa, shugaban jamhuriyar Nijer Bazoum Mohammed yabawa ya yi da jajircewa irin na Dangote wajen gina wannan matatar mai da za ta taimaka wa Najeriya da sauran kasashen Afurka, irin su Nijar da sauran su.

Bazoum Mohamed

Ko mene ne alfanun wannan matatar mai ga Najeriya da sauran kasashen afurka? Dr Babangida jibrin Wushishi masanin harkar hakowa da sarrafa man fetur ne a Najeriya; ya ce ko shakka babu gina wannan matatar man fetur zai taimaka wajen samar da man fetur da kuma daidaita farashinsa a kasa da kuma samar da aikin yi.

Ta fuskar tattalin arziki ma, masana tattalin arziki irinsu Dr Dauda Mohammed Kontagora na cewa; abin yabawa ne ta fuskar tattalin arzikin kasa, samar da aikin yi da kuma bunkasar masana'antun da suka dogara da man fetur.

Manyan baki daga ciki da wajen Najeriya ne suka halarci bikin kaddamar da matatar man fetur din da suka hada da shugabannin kasashen Niger da Senegal da Ghana da Togo da kuma wakilin shugaban kasar Chadi.

Saurari rahoton Babangida Jibrin:

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari Da Shugabannin Afirka Biyar Sun Kaddamar Da Matatar Dangote