Bude Sabbin Rundunonin Soja a Najeriya

Rundunar sojan Najeriya na ci gaba da bude sabbin rundunoni da bataliyoyi a sassa daban-daban na kasar.

Yawan samun tashe-tashen hankula a wasu sassan Najeriya, yasa ake ci gaba da ganin an karfafa rudunonin tsaro a wasu sassa da suka hada da Kudancin jihar Kaduna da Sokoto da Fatakwal da Onicha da kuma Bayelsa.

A cewar babban hafsan sojojin Najeriya Janal Tukur Buratai, kundin tsarin mulkin Najeriya a kwai sashen da ya baiwa soja ikon taimakawa gwamnati musamman ta farar hula, don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ‘kasa.

Janar Buratai ya ce suna bude rudunonin sojan ne a wani bangare na aikin da suke don tabbatar da tsaron cikin gida, da kuma taimakawa jami’an ‘yan sanda a lokacin da suke bukatar hakan.

Masanin tsaro janal Yakubu Usman mai ritaya, wannan mataki na zuwa ne a dai-dai lokacin da ya dace, ganin yawan mutanen da ke a Najeriya ya kamata ace an bunkasa yawan sojoji don bayar da tsaro a ciki da wajen kasar.

Sai dai Kwamrad Nasir Kabir na kungiyar kungiyar Kwadago ta Najeriya, na ganin bubbude sabbin rundunonin ba shine masalaha ba. inda yake ganin dole ne gwamnatin Najeriya ta zauna da duk mutanen da ke tayar da hankali domin jin matsalolinsu da kuma samar da hanyoyin warwaresu.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Bude Sabbin Rundunonin Soja a Najeriya - 2'37"