Kulob din Manchester United da Sporting Lisbon suna ganawa da juna, kan batun sayen dan wasan tsakiya na Sporting mai suna Bruno Fernandes, bisa kudi fam miliyon £60m.
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, tare da mataimakinsa Mike Phelan, sun kalli dan wasan, yayin da ya fafata da FC Porto a ranar Lahadi 5 ga watan Janairu.
Bayan haka dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa, ya zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Vitoria Setuba da ci 3-1 ranar Asabar.
Sai dai a gefe daya kungiyar kwallon kafa ta Sporting da take kasar Putugal, ta ce har yanzu ba'a cimma matsaya ba kan cinikin dan wasan.
Solskjaer ya ce ba zai yi magana a bainar Jama'a ba akan wannan batun, amman dai kulob din na kokari na ganin ya dauko dan wasan da ta dade tana so.
Manchester United tana fama da rashin 'yan wasanta tsakiyarta da suke jinya irin su Paul Pogba da Scott McTominay.