Britaniya Na Niyar Sake Wani Sabon Shirin Ficewa Daga Tarayyar Turai

Ana bukatar sauran kasashe 27 dake mambobin Tarayyar Turai su amince ta kara ma Britaniya wa’adin da ya wuce 29 ga watan Maris na bana.

A yau Alhamis ne Firayin Ministar Britaniya, Theresa May, ke kokarin shawo kan shugabanin kungiyar Tarayyar Turai, a birnin Brussels, domin su amince, da karawa Britaniyar wa’adin watanni uku, abin da zai ba kasar damar gano hanyoyin da zata fita daga tarayyar.

Dole ne sauran kasashe 27, dake mambobin Tarayyar Turai, su amince da duk wani matakin jinkirta ballewa daga tarayyar da zai wuce wa’adin ranar 29 ga watan nan na Maris. Sai dai, ba’a sa ranar ka’da kuri’a akan batun a yanzu ba, har sai mako mai zuwa.

Kafin May ta tashi zuwa Brussels, inda zata bayyana bukatun ta a taron kungiyar ta EU, da ake yi yau Alhamis, ta gabatar, da bukatun a wata wasika da ta aikawa shugaban kwamitin Tarayyar Donald Tusk.

Amma, Tusk ya ce, kara tsawaita wa’adin na wani dan lokaci ba zai yiwu ba sai dai idan ‘yan majalisar dokokin Britaniya sun kada kuri’a a mako mai zuwa don amincewa da sauya sharuddan yarjejeniyar da Britaniya da wakilan Tarayyar Turai suka cimma bayan sun kwashe shekaru biyu suna tattaunawa.