Kungiyar 'yan wasan Flying Eagles basu sami nasara ba a wasan su na farko a gasar cin kofin duniya na FIFA na matasa 'yan kasa da shekru ashirin da haihuwa.'yan wasan sun girbi abinda suka shuka ne a sakamakon rashin kwazon su a wasan su na bayan rabin lokaci, yayin da Brazil tayi masu ci 4 - 2 a filin wasan Taranaki New Plymouth.
Dan wasan Brazil Flor Da Silva ya jefa kwallaye a farkon rabin lokaci da kuma bayan rabin lokaci, yayin da kuma Gabriel Jesus da Boschilla Gabriel su ma sunayen su suka fito a cikin jerin wadan da suka jefa kwallaye a ragar Flying Eagles.
Wanda hakan yayi sanadiyyar baiwa 'yan wasan Brazil damar sake lallasa kulob din na Flying Eagles.
Gabriel ne ya fara jefa kwallo a ragar Flying Eagles cikin mintuna hudu da fara wasan na Najeriya suka mayar da martani da kwallaye biyu daga hannun Isaac da Musa Yahaya.
Amma daga karshe sai kawai suka kasa jure hare haren da 'yan wasan Brazil suke kaiwa ranar Alhamis idan Allah ya kaimu za su kara da 'yan wasan koriya DPR a filin wasan Taranaki New Plymouth suka fafata da Brazil.