Ofishin Shugaban Algeria ya ce dadadden Shugaba Abdul’aziz Bouteflika, zai sauka zuwa ranar 28 ga watan Afirilu, lokacin da wa’adinsa zai cika.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar ta APS, ya yada labaran tun jiya Litinin.
Kafar ta APS, ta ce Shugaba Boutrflika zai tabbatar da ci gaba da dorewar cibiyoyin gwamnati kafin ya sauka.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan shafe tsawon mako guda da aka yi ana ta zanga-zangar nuna bijirewa ga shugaban kasar da gwamnatinsa.
A makon jiya, Hafsan Hafsoshin sojojin Algeria mai karfin fada a ji, ya girgiza kasar bayan da ya yi kiran da a ayyana Shugaba Bouteflika a matsayin mara sukunin iya shugabantar kasar, a kuma saukar da shi.