Kwana guda bayan da dubban ‘yan kasar Algeria suka yi zanga zangar adawa da yunkurin da shugaba Abdelaziz Bouteflika yake yi na neman wa’adi na biyar, shugaban ya nada sabon shugaban gangamin yakin neman zabensa.
Shugaba Bouteflika ya zabi ministan sufurinsa Abdelghani Zaalena wanda zai maye gurbin tsohon firai minista Abdelmalek Sellal a matsayin Darektan gangamin yakin neman zabensa a zaben da ke tafe, kamar yadda wata sanarwa ta nuna, wacce kamfanin dillancin labaran kasar ta Algeria wato APS ya wallafa a jiya Asabar.
A ranar 18 ga watan Afrilu kasar ta Algeria za ta gudanar da zaben shugaban kasa.
A dai shekarar 2013, shugaba Bouteflika mai shekaru 82, ya samu matsalar shanyewar barin jikinsa, lamarin da ya sa ba kasafai ake ganinsa a baina jama’a ba.