WASHINGTON, D.C. —
Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da ke kasar Jamus, ta saye matashin dan wasan gaba na Red Bull Salzburg, mai suna Erling Haaland, akan kudi euro miliyan €20, kwatankwacin fam miliyan £17.1.
Dan wasan dan kasar Norway, mai shekaru 19 da haihuwa, ya amince da komawa kungiyar ta kasar Jamus, bisa yarjejeniyar shekaru hudu, wanda zai kare a shekarar 2224.
Haaland, wanda a da yake ga tsohon dan wasan Manchester City Alf-Inge Haaland, ya zo Salzburg ne daga kulob din Norwegian a watan Janairun 2019.
Ya zura kwallaye 16 a wasanni 14 da ya buga, cikin gasar ta kasar Austria, a wannan kakar wasan bana.
A ranar 3 ga watan Janairun 2020, ne dan wasan zai rattaba hannu a kungiyar ta Borussia Dortmund a hukumance.