Borno: 'Yan Gudun Hijira Sun Koka Kan Karancin Muhalli

'Yan gudun hijira

A cikin makonnan ne Gwamnatin Jihar Borno ta rufe wasu sansanonin 'yan gudun hijira biyu dake cikin garin Maiduguri cikin 27 da ake da su, inda tayi jigilar 'yan gudun hijiran zuwa wani kauye da ake kira Auno dan tsugunanar da su a wasu rukunin gidaji da ta gina guda 580.

Sai dai a iya cewa wannan mataki ya bar baya da kura, ganin irin yadda daruruwan wadannan 'yan gudun hijiran suka kasa samun muhalli.

An dai rufe gidajen 'yan gudun hijarar fiye da 500, da ma na sansanin masu iyi wa kasa hidima na NYSC.

Sai dai wadannan gidajen guda 550 ba su wadace su ba, don yanzu haka ma wasu daga cikin su a waje su ke kwana tun lokacin da aka maida su wannan kauye na Auno.

Yan gudun hijira

Muryar Amurka ta tattauna da wasu daga cikin 'yan gudun hijirar inda suka bayyana halin da suke ciki cewar sun zo ne da niyyar an ce za'a ba su gida.

Amma kuma sun iso an ce masu babu, cewar sun kare. Yanzu haka kwanansu biyu kenan da zuwa inda suke rokon gwamnati da ta taimaka masu, ta kai su inda za su samu dakuna.

Mun kuma tuntubbi gwamnar Borno Umara Babagana Zullum game da makomar wadanan 'yan gudun hijirar da suka ci gaba da kasancewa a waje.

Ya kuma ce akwai doka, kuma wanda ya tashi ya taho, ya kamata ya jira gwamnati, ya ji mai ake ciki.

Gwamnan ya kara da cewa, galibin 'yan gudun hijirar, sun fi so ne su koma garinsu na asali.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Gudun Hijira Sun Koka Kan Karancin Muhalli