BORNO: Wasu Na Yayata Jita-jita Cewa Ana Yiwa ‘Yan Makaranta Wata Allurar dake Haifar da Munanan Cututtuka

Kwamishanan Ilmi na jihar Borno Kanar Musa Kubo

Yayinda gwamnatin Borno ke kokarin farfado da harkokin ilmi a jihar da Boko Haram ta daidaita, sai ga wasu suna yayata jita-jitar cewa ana yiwa yara allura a makarantu har suna kamuwa da cuta, abun da ya tsorata wasu iyaye har suna janye ‘ya’yansu daga makarantun gwamnatI

Gwamnatin jihar Borno ta fayyce jita-jitar da ake yadawa ta kafar sada zumunta ta zamani, wato Facebook, na cewa wasu mutane da ba’a tantance ba suna bin makarantun firamare suna yiwa dalibai allura a kawuna da kuma cibi.

Anyi zargin cewa allurar tana haifar da wasu munanan cututtuka, lamarin da ya sa iyayen yara soma janye ‘ya’yansu daga makarantun gwamnati.

An yi mako guda ana fama da jita-jitar har ma lamarin ya shafi makarantun cikin garin Maiduguri da kewaye.

Yanzu dai hukumomin jihar Borno sun shiga maganar. Kwamishanan ilmi, Kanar Iyo Kubo yace basu ba kowa dama ya shiga makarantu ya yiwa dalibai allura ba. Yace wasu ne kawai suke yayata jita-jitar domin cimma muradunsu.

Shi ma Alhaji Taka Ali Abba, babban sakataren Ma’aikatar Kula Da Makarantun Firamare ta Maiduguri, ya ce ko shi ya karanta a Facebook da WhatsApp cewa an yiwa wata yarinya allura har wani abu ya fita a gabanta. Amma yace duk wannan jita-jita ce kawai. Ya bada tabbacin cewa ba wata makarantar da zata yi wa yara allura ba tare da amincewar gwamnati ba.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

BORNO: Wasu Na Yayata Jita-jita Cewa Ana Yiwa ‘Yan Makaranta Wata Allurar dake Haifar da Munanan Cututtuka - 3' 34"